1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta kada kuri´a kan wata yarjejeniyar da zata kayyade cinikin makamai

October 27, 2006
https://p.dw.com/p/BueG
Wani kwamitin MDD ya ba da damar da a ci-gaba da fasalta wani daftarin yarjejeniya ta kasa da kasa akan cinikin makamai. Burin wannan mataki shi ne a yi gyara ga dokokin da ake amfani da su yanzu wadanda suka yarda a tura makamai yankunan da ake fama da rikici a ciki duk da takunkuman sayar da makamai dake aiki. Kasashe 139 na MDD suka kada kuri´ar amincewa da wannan mataki, Amirka ce kadai ta nuna adawa yayin da China da Rasha suka yi rowar kuri´unsu. Masharhanta sun ce ko da yake za´a dauki shekaru masu yawa kafin a cimma yarjejeniyar, amma kuri´ar wani muhimmin mataki ne akan turbar da ta dace.