1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta kira taron gaggawa kan rikicin Falasdinu

Gazali Abdou TasawaOctober 16, 2015

Kwamitin sulhu na Majalissar Dinkin Duniya ya shirya wani taro a wannan Juma'a domin duba hanyoyin shawo kan sabon rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da Falasdinawa

https://p.dw.com/p/1Gp9c
Westjordanland Hebron Ausschreitungen Gewalt
Hoto: Getty Images/AFP/H. Bader

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na shirya wani taron gaggauwa a wannan Juma'a domin tattauna batun rikicin baya bayan nan da ya barke tsakanin kasar Isra'ila da al'ummar Falasdinawa inda mutane 39 suka mutu a cikin makonni biyu kawai. Wata majiyar diplomasiyya ta ce kasar Jodan ce ta nemi a gudanar da wannan zama.

Da misalin karfe ukku agogon JMT na wannan Juma'a ce komitin sulhun MDD zai soma zaman nasa inda zai tattauna batun .

Sai dai wasu jami'an diplomasiyya da su ka bukaci a sakaya sunayensu sun kwarmata cewa zai wuya taron ya iya daukar wani mataki a wannan karo illa dai kawai zai yiwu ya fitar da sanarwa ta yin kira ga bangarorin biyu na Falasdinawa da Isra'ilar da su dakatar da fadan da suke yi.

A share daya dai illahirin kungiyoyin Falasdinawa ne suka yi kira zuwa ga gudanar da zanga zanga a ko ina a cikin kasar a wannan Juma'a bayan kammala sallar Juma'ar.