1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta koka kan kisan 'yan Rohingya

Ahmed Salisu
September 11, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar kisan da ake yi wa 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar kyakkyawan misali ne na kisan kiyashi.

https://p.dw.com/p/2jjCn
Krise Myanmar - Rohingya-Flüchtlinge
Hoto: Reuters/D. Siddiqui

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya da ke kula kare hakkin dan Adam Zeid Ra'ad Al Hussein ya ce muddin ba a yi da gaske ba to fa kisan da ake yi wa 'yan kabilar ta Rohingya wanda tsiraru ne zai iya kaiwa ga shafesu daga doron kasa. Wannan kalamai na Majalisar ta Dinkin Duniya na zuwa ne daidai lokacin da kasashen duniya da kungiyoyi da ma fitattun mutane ciki kuwa har Archbishop Desmond Tutu da Dalai Lama ke cigaba da yin kiraye-kiraye ga mahukuntan Myanmar musamman ma dai Aung Sang Suu Kyi kan su kawo karshen kisan da ake yi wa 'yan kabilar ta Rohingya.