1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta nemi agajin gaggawa ga Gaza

Yusuf Bala Nayaya
August 30, 2017

Guterres ya yi kira ga bangarorin biyu na Falasdinawa wato Hamas da ke jan ragama a Gaza da Fatah da ke mulkin wasu yankuna a Yamma da Kogin Jodan su hada kai a samu kasa mai ci gaba.

https://p.dw.com/p/2j5ZE
Palästina | Social-Media-Kampagne #SavePalPeople in Gaza
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/M. Faiz

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da babbar murya akai agaji babba ga al'ummar yankin Gaza, yayi kiran ne a wannan rana ta Laraba yayin ziyararsa ga wannan yanki inda ya bukaci a gaggauta sakin Dala miliyan hudu daga majalisar ta kasa da kasa a matsayin kudin tallafin gaggawa.

Da yake jawabi a wata makaranta da ke samun goyon bayan MDD a Arewacin na Gaza, Guterres ya yi kira ga bangarorin biyu na Falasdinawa wato Hamas da ke jan ragama a Gaza da Fatah da ke mulkin wasu yankuna a Yamma da Kogin Jodan su hada kai a samu kasa mai ci gaba.

Ziyarar ta Guterres da ke zama ta farko tun bayan hawansa sakataren na MDD a farkon wannna shekara ya gana da shugabannin na Falasdinawa da bangaren Isra'ila inda yake da buri na sake  komawa teburin tattaunawa don samun zaman lafiya a yankin.