1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta samu izinin kai kayan agaji a Siriya

Gazali Abdou TasawaJanuary 8, 2016

Gwamnatin Siriya ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Red Cross izinin kai kayan agaji a wasu biranan kasar inda yaki ya rutsa da mutane tare da sakasu cikin matsalar yinwa.

https://p.dw.com/p/1Ha5C
Symbolbild Rotes Kreuz in Aden, Jemen
Hoto: Getty Images/AFP/M. Huwais

Gwamnatin kasar Siriya ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar agaji ta Red Cross izinin kai kayan agaji a wasu biranan kasar wadanda yaki ya rutsa da mutane a cikinsu tare da sakasu cikin matsalar yinwa a 'yan watannin baya-bayan nan.

Ofishin Hukumar kula da aiyyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya wato OCHA ya ce biranan kasar ta Siriya da ke fama da wannan matsala da kuma za su ci moriyar agajin sun hada da birnin Madaya da ke a hannun 'yan tawaye da amma sojojin gwamnatin Siriya suka yi masa kofar raggo yau tsawon watanni shida, da kuma biranen Foua da Kafraya na 'yan Shi'a masu kunshe da mutane kimanin dubu 20 wadanda su kuma 'yan tawaye suka yi masu kawanya tare da saka al'ummar cikin yanayin yinwa da karancin magunguna.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniyar ta bayana gamsuwrta da wannan izini da ta samu kuma ta ce za ta soma aikin shiga da kayan agajin ba tare da bata lokaci ba.