1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta tsayar da waádi na cimma yarjejeniyar sulhu a Dafur

April 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2H

Kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya ya baiwa gwamnatin Sudan da yan tawayen ƙasar dake faɗa da juna a lardin Dafur waádi su gaggauta cimma yarjejeniyar sulhu nan da 30 ga wannan watan na Aprilu. Ita ma ƙungiyar gamaiyar Afrika wadda ta shiga tsakani domin sasanta ɓangarorin biyu, a tarukan shawarwarin sulhu da ta gudanar a birnin Tarayyar Nigeria Abuja, ta tsayar da waádi zuwa karshen wannan watan ga bangarorin su cimma yarjejeniya ta dorewar zaman lafiya a tsakanin su. Tarzoma ta ɓarke ne a Dafur a shekarar 2003, bayan da alúmomin yankin waɗanda ba jinsin larabawa ba ne, suka bujirewa gwamnatin bisa zargin maida su saniyar ware. Gwamnatin ta maida martani tare da kafa kungiyar banga ta janjaweed wadda ta aikata taása ta kisan dubban jamaá da kuma sanya wasu mutanen kusan miliyan biyu gudun hijira. Ana sa ran nan ba da jimawa ba gwamnatin Britaniya za ta fitar sunayen wasu mutane waɗanda ta haƙiƙance sune ke hana ruwa gudu a yunƙurin da ake na samar da wanzuwar zaman lafiya, domin majalisar dinkin duniya ta ɗauki matakan ladabtarwa a kan su. A waje guda kuma sakataren majalisar ɗinkin duniya Kofi Annan ya baiyana damuwa da ɓarkewar faɗa a kan iyakar Chadi da Sudan.