1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi Allah wadai da harin Kunduz

Usman Shehu UsmanAugust 22, 2017

Farmakin da Amirka ta kai wa wani asibitin kungiyar Doctors Without Borders a Afganistan inda ta hallaka mutane 19 wasu 37 suka jikkata lamari ne na aikata alaifin yaki

https://p.dw.com/p/1Er0X

A cewar daraktan gudanar da ayyukan asibitin Bart Janssens, abun kaico shi ne sojojin Amirka da na Afganistan duk an fada musu ana kai wa asibitin hari amma sama da mintuna 30 Amirkawan suka ci gaba da luguden wuta kan. Daraktan asibitin mai bada agajin gaggauwa kyauta ya ce wannan asibitin ya yi shekaru hudu ya na aiki a Kunduz kuma ba karamin asibiti ba ne domin girmansa ya fi filin kwallon kafa fadin kuma sau da dama suka yi magana da masu gaba da juna kan asibiti. Don haka ya ce kungiyar ta Doctors Without Borders ba za ta taba lamunta ace wai kuskure ne Amirka ta yi ba.