1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi kiran kwantar da hankali a kasar Iraqi

February 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv77

Kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya ya bukaci alúmar ƙasar Iraqi su nuna hakuri da sanin ya kamata, bayan harin bom ɗin da aka kai a ɗaya daga cikin tsarkakan wuraren ibada na mabiya shiá. Dubun dubatan jamaá sun gudanar da zanga zanga a sassan ƙasar bayan aukuwar harin bom ɗin wanda aka zargi cewa wasu yan takife ne daga bangaren yan sunni aikata kai harin. Harin bon ɗin wanda ya lalata hasumiyar masallacin al-Askari dake birnin samara ya haddasa daukar fansa inda yan shiár suka kai farmaki tare da ƙona masallatai da dama na yan sunni wanda kuma ya kai ga hasarar rayukan mutane shidda. Jagoran addini Ayatollah Ali al-Sistani ya yi kiran da a kwantar da hankula tare kuma da zaman makoki na mako guda. Shugaban ƙasar Iraqin Jalalal Talabani ya ja hankali da cewa yan takifen na neman haddasa yakin basasa a tsakanin alúmar kasar.