1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD za ta kiyaye zaman lafiya a Burundi

Mouhamadou Awal BalarabeApril 2, 2016

Majalisar Dinkin Duniya na shirin turawa da dakarun da za su kiyaye zaman lafiya a Burundi sakamakon rikicin siyasa da ake fama da shi a kasar.

https://p.dw.com/p/1IOME
New York UN-Sicherheitsrat Sitzung
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Franklin II

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudiri da zai bada damar turawa da jami'an 'yan sanda Burundi, don kiyaye zaman lafiya da ke tangal-tangal a wannan kasa. Babban Sakataren majalisar Ban Ki-Moon ne aka kayyade ma wa'adin kwanaki 15 don nazarin yadda zai aiwatar da wannan kudiri.

Idan dai za a iya tunawa kasar Burundi ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya nace kai da fata sai ya yi tazarce, duk da cewar kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa tsayawa takara. Fiye da mutane 400 ne suka rasa rayukansu a wannan rikici, yayin da wasu dubbai kuma suka kaurace wa matsugunansu.

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya Francois Delattre ya ce kasarsa ta shigar da wannan daftari ne saboda ta zaku da ganin cewar an samu zaman lafiya a Burundi.

Ya ce "Faransa ta yi imanin cewar dole ne Majalisar Dinkin Duniya ta dauki duk matakan da suka wajaba don ganin cewar ta kawo karshen rikici a kasar Burundi. Wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan kwamitin Sulhu na taimaka wa 'yan Burundi dinke bararakar da ke tsaninsu."