1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD za ta rage yawan dakarunta a Kwango

March 31, 2017

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'a da gaggarumin rinjaye na amincewa da rage addadin dakarun rundunar wanzar da zaman lafiya na Majalisar a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/2aTeL
Demokratische republik Kongo UN Friedensmission Monusco
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

 Wakilan kwamitin sulhu sun kada kuri'ar rage yawan dakarun rundunar da kishi bakwai cikin dari  wanda daga addadin sojojin da jami'an tsaro dubu 19 da 'yan ka  da ake da su a Kwangon ,ya koma dubu 16.Gesine Ames wata 'yar kasar Jamus  kwararrariya a game da yankin tsakiya na Afirka ta ce akwai bukatar tura dakarun na MONUSCO zuwa Kwangon domin tabbatar da tsaro a yankunan da ake yin tashin hankali.