1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mene ne banbancin Kotun Duniya da kuma Kotun Shari’ar Miyagun Laifuka ta Duniya

September 10, 2009

Taƙaitaccen bayani akan banbancin da ke tsakanin Kotun Duniya wato ICJ da kuma Kotun Shari’ar Miyagun Laifuka ta Duniya wato ICC.

https://p.dw.com/p/JcQW
Tambarin Kotun Shari’ar Miyagun Laifuka ta Duniya "ICC".

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon mun same ta ne daga hannun Malam Aƙilu Abdulƙadir daga ƙasar Kamaru, ya ce shin mene ne banbancin da ke tsakanin Kotun Duniya wato ICJ a taƙaice, da kuma Kotun Shari'ar Miyagun Laifuka ta Duniya wato ICC a taƙaice.

Amsa: Duk da cewa dukkanin kotunan guda biyu wato Kotun Shari'ar Miyagun Laifuka ta Duniya da Kotun Duniya suna da mazauninsu ne a birnin Hague, na ƙasar Holand, amma akwai banbanci a tsakaninsu ƙwarai da gaske. Ita Kotun Duniya ba ta da hurumin hukunta waɗanda suka aikata manyan laifuka. domin Ita kotu ce ta sasanta rikici ko kuma warware wata taƙaddama tsakanin ƙasashen duniya. Akan abin da ya shafi rikicin kan iyaka ko na kasuwanci da dai sauransu. Sannan kuma ita wani reshe ne na cibiyoyin shari'a a Majalisar Dinkin Duniya.

Internationaler Gerichtshof in Den Haag
"Peace Palace" kenan, fadar da acikinta ne Kotun Duniya take.Hoto: Internationaler Gerichtshof

Ita kuwa Kotun Shari'ar Miyagun Laifuka ta Duniya an kafata ne a ƙarƙashin wata yarjejeniya da ake kira "Yarjejeniyar Rome": A ƙarƙashin wannan yarjejeniya dai Kotun Shari'ar Miyagun Laifuka ta Duniya na da hurimin yin hukunci akan laifuffukan da suka shafi kisan ƙare dangi da laifuffukan da suka shafi yaƙi, da na take haƙƙin bil Adaman da aka aikata tun daga lokacin da kotun ta fara aiki a shekara ta 2002. Kuma ba ta da wata alaƙa da Majalisar Ɗinkin Duniya.

Germain Katanga im Internationalen Strafgerichtshof
Germain Katanga, a hannun dama, lokacin da yake fuskantar tuhuma a Kotun Shari'ar Miyagun Laifuka ta Duniya.

Sannan kuma ƙasashe ne kaɗai su ke kai ƙarar matsalolinsu gaban Kotun Duniya , kuma ita Kotun Duniya ba ta ɗora alhakin aikata laifi a kan wata ƙasa, sai dai kawai ta sasanta ta baiwa wadda take gani ita ce da gaskiya, gaskiyarta. Kuma dole ne sai da amincewar dukkanin ƙasashen da ke cikin rikici da juna sannan Kotun Duniya za ta yi hukunci a tsakaninsu. Kuma dole ƙasashen su yarda da cewa duk hukuncin da Kotun Duniya ɗin ta yi a tsakaninsu to ba makawa za su amince da shi. Alal misali sasanta rikicin yankin Bakassi tsakanin Najeriya da Kamaru, inda Kotun Duniya ta yanke hukuncin ba da wannan yanki na Bakassi ga Kamarun. Dole kuma Najeriya ta amince da wannan hukunci, tun da ta yi alƙawarin amincewa da duk hukuncin da aka yanke tun da farko.

Niederlande UN-Gerichtshof Massaker von Srebrenica war Völkermord
tsarin yadda ake zama a cikin Kotun DuniyaHoto: AP

Ita kuwa Kotun Shari'ar Miyagun Laifuka ta Duniya yarjejeniyar haɗaka ce tsakanin ƙasashen duniya da dama. Kuma waɗanda suke da ikon gabatar da ƙara a gabanta sun haɗa da duk wani da ya ke jin cewa an zalunce shi ta fuskar laifuffukan da kotun take da hurumin yanke hukunci akansu, sannan kuma kwamitin sullhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ma zai iya gabatar da ƙara a kotun, sai kuma shi mai gabatar da ƙara na kotun ta Shari'ar Miyagun Laifuka ta Duniya, shi ma yana da ikon sanya kotun ta tuhumi wani. Sannan kuma ga laifuffukan da take da hurumin sauraron su, Kotun Shariar Miyagun Laifuka ta Duniya za ta iya tabbatar da laifi akan wani ta kuma yanke masa hukuncin ɗauri a gidan yari.

Mawallafi: Abba Bashir

Edita: Umaru Aliyu