1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mene ne tarihin ƙasar Kambodiya

Bashir, AbbaSeptember 10, 2008

Taƙaitaccen tarihin ƙasar Kambodiya

https://p.dw.com/p/FFcL
Firaministan ƙasar Kambodiya Hun SenHoto: picture-alliance/ dpa

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito ne daga hannun malam Ahmadu Yarima daga Jihar Kano a tarayyar Nigeria; Mallam Ahmad ya ce, don Allah DW ku ba ni tarihin ƙasar Kambodiya, shin yaya tsarin zaɓen shugabancin ƙasa ya ke a wannan ƙasa?

Amsa: Ita dai Kambodiya wata ƙasa ce da ke kudu maso gabashin Asiya kuma ta na da jama'a da yawansu ya haura miliyan 13. Sunan babban birnin ƙasar Phnom Penh. Kambodiya ta samo asali ne daga daular Hindu da Buddha, wadda ta mulki yankunan Indonesiya da China tsakanin ƙarni na 11 zuwa ƙarni na 14.

Yawancin ‘yan ƙasar Kambodiya mabiya addinin Buddha ne, amma kuma akwai musulmi da dama da chinese ‘yan asalin

ƙasar, da yan asalin ƙasar Vietnam da kuma yan tsirarun yarurruka da ke zaune akan tsaunuka.

Ƙasar Kambodiya na maƙwabtaka da ƙasashen Thailand a yammaci da kuma yamma maso arewa, Laos a arewa maso gabas da Vietnam a gabas da kudu maso gabas. A kudu tana fuskantar kogin Thailand.

Siyasa a ƙasar Kambodiya ta kafu ne akan tafarkin kundin tsarin mulkin ƙasar na 1993, kuma tsari ne da aka yi da ke da Sarki da kuma Firaminista, waɗanda wakilan jama'a ne ke zaɓansu. Firaministan ƙasar shi ne shugaban gwamnati, wadda ta ƙunshi jam'iyyu dabam-dabam, a yayin da kuma sarki shi ne shugaban ƙasa. Sarki ne ke naɗa Firaminista tare da shawara da kuma yardar majalisar ƙoli ta ƙasar. Firaminista tare da ministocin sa na da ikon zartar da doka a gwamnati, a yayin da alhakin tsara dokoki ya rataya ne akan majalisun dokoki da kuma ɓangaren masu zartar da dokar.

A ranar 14 ga watan Oktoba, wata majalisa ta musamman mai wakilai 9, ta zaɓi Sarki Norodom Sihamoni, a wani tsari na zaɓe da aka yi cikin gaggawa, sati ɗaya bayan Sarki Norodom Sihanouk, ya ƙi amincewa. Zaɓen sarki Sihamoni ya sami albarkacin Firaminista Hun Sen da shugaban majalisar dokokin ƙasar, Norodom Ranariddh, waɗanda dukkan su wakilai ne a majalisar zaɓen sarki. An rantsar da sabon sarkin ne a ranar 29 ga watan Oktoba, a babban birnin Kambodiya, wato Phnom Penh.

Masana'antun ƙasar Kambodiya dai sune na sutura, yawon shaƙatawa da kuma gine-gine. A shekara ta 2007, yawan baƙin da suka ziyarci ƙasar daga ƙasashen waje ya haura miliyan biyu. An gano mai da albarkatun ƙasa a ƙarkashin ruwan dake zagaye da ƙasar a shekara ta 2005, kuma idan aka fara zaƙulo waɗannan albarkatun ƙasa a shekara ta 2011, to ana ganin cewa kuɗin shigan da za a riƙa samu daga Man zai haɓaka arziƙin ƙasar ta Kambodiya.