1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Menene ma’anar Boxing Day

Abba BashirDecember 15, 2005

Takaitaccen bayani game da Boxing Day

https://p.dw.com/p/BvVh
Boxing Day a Kasar Sydney
Boxing Day a Kasar SydneyHoto: AP

Masu sauraronmu assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Mr Joshuwa Daudu mazauni a garin Jos a Jihar Pilato ta tarayyar Nigeriya. Maisauraron ya ce yana so asanar da shi dalilin da ya sa ake kiran ranar kashegarin kirsimeti da suna “Boxing Day “.

Amsa: Kamar yadda kundin tattara bayanai na duniya wato“World Book Encyclopedia’’ ya nunar , ya tabbatar da cewa bikin al’ada na kashegarin kirsimeti da aka fi sani da suna“Boxing Day “ a turance, ya samo asali ne daga kalmar Turanci ta (Box) wato Akwati kenan a hausance. Kowa dai yasan yadda a zamanin da dai akwati ya ke a matsayin wajen ajiyar abubuwan da mutum ya mallaka, tun daga abinda ya shafi kudi sutura da dai sauran su. To sakamakon ware wannan rana a matsayin ranar da mutane suke ba da abubuwan da suka mallaka, a cikin akwatunansu, ya sa ake kiranta da suna ranar mika akwatuna.wato “Boxing Day“ a turance. Wannan kuwa ya kunshi bayar da kudi da kuma sauran kyaututtuka ga mabukata,da hukumomi ma su kula da gajiyayyu da kuma tallafawa kananan yara. Wani lokaci wasu mutanen kuma sukan bayar da kyauta ga ma’aikatan gidan aikawa da wasiku ko kuma su sadaukar da wannan rana suna masu bada kyata da sadaka ga duk wanda Allah ya kawo garesu.

Har ila yau dai, kundin ya ci gaba da cewa,kodayake ita wannan ranar hutu da ake kira“BoxinG Day’’ za’a iya bin diddigin asalinta tun daga tsakiyar shekaru na 400-1500 a shekarar miladiyya.Amma dai a gaskiyar magana, haryanzu ba’a samo sahihin asalin wannan rana ba.Domin kuwa akwai hasashe da kuma ra’ayoyi da dama a game da asalin samuwar wannan rana, amma dukkaninsu sun tattarane akan batun ba da akwatuna wato „“Boxes“a Turance,da kuma batun bada kyaututtuka da taimakawa marasa galihu.

Ita dai wannan rana ta Boxing Day wadda kuma take kasancew a kashegarin kowacce rana ta kirsimeti a duk shekara, ta zo dai-dai da ranar da aka ware a addinin kirista a matsayin ranar tunawa da waliyinnan na addinin kirista wato“Saint Stephen’s Day’’ a Turance. Kodayake wasu bangarori basa bambance wadannan bukukuwa guda biyu, amma dai bisa ingantattun bayanai wadannan bukukuwa guda biyu da suka hadu a rana guda, kowannensu zaman kansa ya ke yi, kuma ana gudanar da bikin kowannensu akan al’adu daban-daban da kuma tsarin gudanarwa daban-daban.