1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel a Afrika ta kudu

October 5, 2007

Shugabar gwmanatin jamus ta cigaba da rangadin aikinta a Afrika

https://p.dw.com/p/BtuT
Angela Merkel da shugabannin Afrika
Angela Merkel da shugabannin AfrikaHoto: AP

Bayan kammala tattaunawarta da magabanta kasar Habasha,shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta isa birnin Pretorian kasar Africa ta kudu da yammacin jiya,inda zata gana da shugaba Thabo Mbeki da an jima kadan.

A wannan tattautawar da zata gudana tsakanin Merkel da Thabo Mbeki dai,ana saran karin matsin lamba wa gwamnatin yankin kudancin Afrikan adangane da daukan tsauraran matakai kan shugaba Robert Mugabe na kasar Africa ta kudu.

Gabannin wannan ziyara dai,jamian gwamnatin jamus sun bayyana cewar Merkel,zata tattauna batutuwan kawo sauyi a nahiyar ta Africa ,da kuma dangantakar kasashen nahiyar da tarayyar turai,musamman kana matsalar Zimbabwe.

A jawabin da tayi a headquatar kungiyar gamayyar Africa jiya a Adisa baba,shugabar gwamnatin jamus din tayi kira ga dukkannin kasashen Africa dasu tursasawa shugaba Robert Mugabe adanbgane da cigaban take hakkokin biladama da akeyi a kasarsa.

“tace manufofimmu na ketare sun hadar da yaki da yunwa da talauci,da kokarin shawo kan matsalolin rashawa da cin hanci ,da mulkin danniyya tare tabbatar da hakkin jamaa.Matsalolin da kasar zimbabwe take ciki wani mummunan misali ne,kuma dole ne a dauki matakai da suka dace na shawo kan wannan matsala.Wannan kuwa hakki ne daya rataya a wuyan Kasashen dake makwabtaka Zimbabawe,musamman Africa ta kudu.”

A yanzu haka dai kasar ta Zimnbabawe na fama da matsalolin rayuwa,sakamakon durkshewar tattalina arikinta .

A hannu guda kuma shugaba Thabo Mbeki yana aiwatar da diplomasiyya na kyaliya akan Robert Mugane ,kuma shine mai shiga tsakanin jammiyyar Znanu PF mai mulki da kuma babbar jammiiyar Adawa ta MDC dake kasar ta Zimbabwe.

“Mbeki yace yana da matukar muhimmanci aga ainihin halin da Africa take ciki,domin hakan ne kadai zai iya bada damar sanin ainihin matsayinta da halin da take ciki”

Angela Merkel wafdda ta sanya fifiko akan yaki da talauci a Afrikaa a yayinda take shugabancin kungiyar kasashe masu cigaban masanaantu ta G-8,taki bin sawun prime ministan Britanni Gordon Brown akan matsayin da ya dauka kan shugaba Robbert Mugabe na Zimbabwe.

Brown dai yayi barazanar kauracewa taron hadin gwiwan Africa da kasashen turai da zaa gudanar a birnin Lisbon,idan har shugaban Zimbabwen zai halarci wannan taro.Akan wannan hali da ake ciki kuwa shugabbannin kasashen Africa na shirin kin halartan wannan taro ,idan bazaa amincewa Mugabe ya halarta ba,taron dake da nufin gano bakin zaren warware matsalolin dake addabar kasashen na Africa.

ABayan ganawar tasu a yau da shugaba Mbeki dai,anasaran Merkel zata yi rangadin wuraren da ake aiki,dangamne da gasar cin kofin duniya ta 2010,da Africa ta kudun zata zame mai masaukin