1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta kai ziyara yankin Balkan kan shigarsu EU

Jamila Ibrahim Maizango/ MNAJuly 9, 2015

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna goyon baya ga hankoron kasashen yankin Balkan na shiga kungiyar Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/1Fw29
Angela Merkel mit Mladen Ivanic
Hoto: Reuters/A. Bronic

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za ta taimaka wa Bosniya da ke sahun karshe a jerin kasashen yankin Balkan da ke son shiga kungiyar Tarayyar Turai, ta gaggauta shirye-shiryen samun wakilci a kungiyar ta EU. Merkel wadda ke halartar bikin cika shekaru 20 da kisan kiyashin Srebrenica lokacin da sojojin Sabiyawan Bosniya suka kashe Musulmi dubu takwas ta ce akwai matsaloli a Bosniya da ya kamata a warware tukuna.

"Muna goyon bayan muradun dukkan kasashen yankin Balkan game da Turai, mun kuma san da matsaloli da yawa da ya kamata a warware su a Bosniya. Yankin gaba daya zai bunkasa ne idan Bosniya ta samu kyakkyawan cigaba."

A bara Jamus da Birtaniyya sun kaddamar da wani shirin farfado da burin Bosniya na shiga kungiyar EU, inda suka mayar da hankali kan sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa maimakon batutuwan da suka raba kan 'yan siyasar kasar.