1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta goyi bayan matakan hukunta matasa masu aikata laifuka

January 5, 2008
https://p.dw.com/p/Ckin

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta amince da wasu tsaurarran matakai da ake iya dauka don hukunta matasa masu aikata miyagun laifuka. A lokacin da take jawabi a birnin Wiesbaden, Merkel, tace babu shakka, matasa ‚yan ƙasa da shekaru 21 da haifuwa, ke da alhakin aikata kusan kashi 50 cikin dari na laifukan da ake aikatawa nan Jamus, kuma da yawa daga cikinsu baki ne. Kana, ta bayyana goyan baya ga kiran da gwamnan jahar Hesse Roland Koch ya yi na a kirkiro wani shirin da zai tilasta korar baƙi masu aikata miyagun laifuka daga ƙasar. Koch mai neman sake tsayawa takarar kujerar shugabancin wannan jahar, ya sanya wannan batu kann gaba a kampen ɗinsa. Hukumomin Jamus sun fara bada ƙarfi kann batun ɗaukan wasu matakan tsaro, bayan wasu matasa biyu, ‚yan asalin Turkiya da Girga sun kaiwa wani tsoho hari a tashar jiragen ƙasa dake birnin Munich a makwannin baya.