1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

280810 merkel pakistan hilfe

August 28, 2010

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta buƙaci Jamusawa su bada gudunmawar agaji ga Pakistan.

https://p.dw.com/p/OybY
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a sakonta na mako mako da ta gabatar a ranar Asabar ga al'umar ƙasa wanda kuma aka yaɗa ta akwatunan Talabijin ta yi kira ga Jamusawa su ruɓanya taimakon jin ƙai domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta yiwa ta'adi a Pakistan. Merkel kuma ta yi watsi da fargabar da wasu ke baiyanawa cewa taimakon ba za su kai ga mutanen da aka yi domin su ba saboda matsalar cin hanci da ta yi katutu a tsakanin mahukuntan na Pakistan. 

Shugabar gwamnatin Angela Merkel wadda sakonta ya maida hankali akan Pakistan da halin da jama'ar kasar ke ciki, ta baiyana ambaliyar ruwan da aka fuskanta a Pakistan ɗin da cewa shine mafi muni da aka taɓa gani a tsawon tarihin ƙasar.

" Yan kwanakin da suka wuce dukkaninmu mun ga hotuna na matsanancin hali da Pakistan ta sami kanta a ciki. Mun ga yadda ruwa ya mamaye yanki wanda girmansa ya kai rabin faɗin ƙasar Jamus inda kuma mutane kimanin miliyan goma sha biyar suka tagaiyara".

Merkel ta ce Pakistan ita kaɗai ba za ta iya shawo kan wannan matsalar ba. Tilas ta na buƙatar taimako, wannan ƙalubale ne babba mu taimaka mata domin sake gina ƙasar.

Flutkatastrophe in Pakistan
Tallafin abinci ga iyalai da suka yi ƙaura saboda ambaliyar ruwa a PakistanHoto: AP

" Don haka gwamantin Jamus ta bada taimakon agaji na euro miliyan 25, tare da ƙungiyar tarayyar Turai gaba ɗaya mun bada tallafin euro miliyan 70. To amma duk da haka ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba, ƙungiyar tsaro ta NATO za ta ɗauki nauyin jigilar kayayyakin agaji waɗanda suka haɗa da magunguna da abinci zuwa yankunan da ba'a samu an isa gare su ba domin kaiwa jama'a taimako".

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta ce abu ne mai matuƙar muhimmanci jama'a su taimakawa wannan yunƙuri na gwamnati da dukkan abin da za su iya bayarwa. Ta kuma yi godiya ga mutanen da suka bada tasu gudunmawar tana mai cewa " Ina godewa dukkan waɗanda suka rigaya suka bada taimako, ga waɗanda kuma basu bayar ba kuma ina kira su sake nazari na dacewar bada taimakon ga Pakistan".

" Merkel ta ƙara da cewa ta san jama'a da dama suna da shakku da tunanin cewa anya shin kuɗaɗen da ake bayarwa suna isa ga mutanen da aka yi taimakon domin su kuwa ? a saboda haka tace

" Wannan tabbas a don haka ne ma ƙungiyoyi masu zaman kansu na nan Jamus suke danka taimakon kai tsaye hannu da hannu ga mutanen da ambaliyar ta shafa, kuma tuni rukunin farko na agajin da muka aika Pakistan ya isa ga mutanen kuma ya taimaka matuƙa, saboda haka yake da muhimmanci mu haɗa hannu da taimakon gwamnati dana sauran jama'a domin mu ƙara tallafawa". Shugabar gwamnatin ta kuma yi tambayar ko jama'ar sun san dalilin da ya sa yake da muhimmanci Jamus ta taimakawa Pakistan ?

" Pakistan maƙobciya ce ga ƙasar Afghanistan, yankunan da a yanzu ruwa ya mamaye, yanki ne da yan al-Qa'ida dana Taliban suke da ƙarfi suke kuma gudanar da ayyukansu, saboda haka wajibi ne gamaiyar ƙasa da ƙasa tare da jama'ar Pakistan su yi dukkan abin da ya dace na taimako domin kaucema wani abu da zai  tauye cigaban da muka samu sannan kuma da ganin ba a bar matsalar ta zamo gawurtacciya ba".

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta ce zai ɗauki dogon lokaci kafin Pakistan ta mayarda hasarar da ambaliyar ruwan ta haifar, a saboda haka ta nanata kira ga Jamusawa su ƙara taimakawa a'umar Pakistan.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Halima Balaraba Abbas