1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel zata ziyarci Izraela da ministocin ta

Zainab Mohammed March 15, 2008

Ziyarar shugabar gwamnatin Jamus a kasar Izraela

https://p.dw.com/p/DOwR
Steinmeier da MerkelHoto: picture-alliance/ dpa
A gobe lahadi ne Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ke fara wani rangadin aiki a Izraela,wanda ke zama na ukun irinsa da hawa kan karagar mulki.Merkel zata zama shugabar gwamnatin Jamus ta farko datayi jawabi a gaban majalisar dokokin Izraelan ta Knesset,sama da shekaru 60 da kawo karshen yakin duniya na biyu. Merkel dake zama shugabar gwamnatin Jamus ta farko da aka haifa bayan yakin duniya na biyu,zata je ƙasar Izraelan ne da manyan ministocin gwamnatin kasar,inda zaa tattauna dangantakar bangarorin biyu. A baya dai Jamus ta gudanar da irin wannan tattaunawa da kasashen Faransa da Italiya da Spain da Rasha da Poland.Ana kuma saran cewar majalisar zartarwar Izraela zata gudanar da ziyara makamancin hakan a shekara ta 2009. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier wanda ke cikin tawagar ta shugabar gwamtin na jamus yace..... "Muna muradin ganin cewar dangantaka ya ingantu tsakaninmmu da Izraela.Dangane da hakane zamu wannan tattaunawa tsakanin gwamnatocin kasashen biyu.Kuma a ganina wannan wata dama ce wa ɓangarorin biyu da zasu samu cigaba,wanda zasu aiki tare domin ingantuwan dangantaka" Da saukarta a Izraelan dai Angela Merkel zata kai ziyara Sde Boker,dake cikin sahara,wurin da primiyan Izraela na farko David Ben Gurion ya gana da shugaban gwamnatin Jamus na yamma na farko Konrad Adenauer a 1966,kuma nan ne aka binne shi bayan mutuwar sa. Ziyarar ta shugabar gwamnatin Jamus din dai tazo ne adaidai lokacin da Izraelan ke shirin gudanar da bukin cika shekaru 60 da kafuwa a watan mayu. Jakadan Izraela a Berlin Yoram Ben-Zeev,yace wannan itace ziyara mafi muhimmanci da wani shugaban gwamnatin jamus ya tabayi zuwa Izraela. Tsohon ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya taba fadi cewar sakamakon kisan kiyashi da akayiwa yahudawa,bai yi tsammani akwai wata dangantaka da zata shiga tsakanin su ba. Amma sama da shekaru 60 da wayewar kai dangane da abubuwanda suka faru a baya,Jamus ta kasance kasa mafi muhimmanci a nahiyar turai a idanun Izraela ta fannin siyasa da kasuwanci,idan ka dauke Amurka. Duk dacewar Merkel na muradin ganin cewar Jamus ta taka muhimmiyar rawa a kokarin cimma zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya,manazarta sunyi nuni dacewar wannan ziyarar zata mayar da hankali ne kan dangantakar Izraela da jamus. A ranar talata nedai shugabar gwamnatin jamus din zatayi jawabi a gaban majalisar dokokin Izraela ta Knesset na tsawon mintuna 20.