1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Michel Niaucel ya rasu a Cote d´Ivoire

Yahouza S.MadobiFebruary 7, 2007

Wasu mutane a Abidjan sun kashe jami´in EU Michel Niaucel

https://p.dw.com/p/BtwL

Wannan jami´in diplomatia, mai suna Michel Niaucel, ɗan assulin ƙasar France ne, ma´aikacin ƙungiyar tarayya turai ,a ƙasar ta Cote d´Ivoire.

Wasu mutane ne ,da har yanzu ba tantance ba, su ka yi masa dura mikiya a gidan sa dake birnin Abidjan, inda nan take su ka halaka shi.

Niaucel, ya je Cote D´Ivoire tun shekara ta 2002, inda ya ke kulla da fannin tsaro.

Bayan barkewar rikicinkasar ya na daga fansawa da su ka koma gida adalili da rashin kwaciyar hankali, kaminya dawo a shekara ta 2005.

Cemma yan assulin ƙasar France, da ma wasu daga baƙin turawa dake zaune a ƙasar, na fuskantar barazana, daga magoya bayan shugaban ƙasa Lauran Bagobo dake zargin ƙasashe turai da ɗaurewa yan tawaye gindi.

A sanarwar da ya hiddo yammacin jiya, shugaban ƙungiyar gamayya turai, Jose Manual Barroso yayi tur da Allah wadai da wannan kissa , ya kuma issar da kira ga hukumomin Abidjan, su buda bincike na haƙiƙa, tare da haɗin gwiwar opishin jikadancin France a Abidjan , domin gano masu alhakin wannan ɗanyan aiki,a kuma gurfanar da su gaban kotu.

Itama komishinar EU, mai kulla da harakokin ƙetare, Ferrero Waldner, ta bayyana juyayi da wannan rashi, ta kuma nuna matsanacin hali da jami án ƙungiyar taraya turai ke aiki, a ƙasar Cote D´Ivoire, tun bayan ɓarkewar rikicin tawaye.

Wannan kissa ya zo daidai lokacin da, tawagogin gwamnati da na yan tawayen Cote d´Ivoire su ka fara tantanawa, a birnin Ouagadougou, na Burkina Faso, bisa shiga tsakanin shugaba Blaise Compaore.

A jiya talata Compaore, ya gana da ɓangarorin 2 daban-daban, inda ko wane ya gabatar masa a rubuce da shawawarin kawo ƙarshen taƙƙaddamar.

Nan gaba a yau ne kuma, za a shiga kwana na 2, na wannan taro.