1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miliyoyin mutane a Africa na cikin matsalolin yunwa

Ibrahim SaniJanuary 17, 2006

Yunwa na yiwa miliyoyin mutane a wasu kasashe na Africa barazana

https://p.dw.com/p/BvU0

Ya zuwa yanzu dai hukumar bada tallafin abinci ta Mdd, ta kiyasta cewa akwai mutane kusan miliyan goma sha daya a yammacin kasashen Africa dake bukatar tallafin abinci a cikin wannan shekara ta 2006.

Rahotanni sun shaidar da cewa,wannan matsala ta biyo bayan matsaloli ne na rashin kyakkyawar damina da da yawa daga cikin kasashen na yammacin Africa suka fuskanta a shekarar data gabata.

Daya daga cikin kasashen da suka fi fuskantar wannan matsala kuwa a cewar hukumar bada tallafin abincin ta Mdd, itace kasar Niger.

Duk da damina mai kyau da kasar ta Fuskanta a karshen shekarar 2005, hukumar ta Mdd tace a yanzu haka akwai mutane kusan miliyan uku da yunwa kewa barazana a kasar ta Niger.

A yanzu haka a cewar hukumar ta Mdd, tana nan tana gwagwarmayar bawa ire iren wadannan mutane tallafi na abincin a janhuriyar ta Niger.

A kasar ta Niger kadai a cewar hukumar ta Mdd, akwai bukatar tsabar kudade har dalar Amurka miliyan 22 don inganta aiyukan ta na bada tallafi a kasar ta Niger.

Bugu da kari hukumar ta Mdd, ta kara da cewa akwai kuma wasu mutane a kalla miliyan shida da yunwar kewa barazana a wasu kasashe na gabashin nahiyar ta Africa, a sakamakon fari da suka fuskanta da kuma rashin inganci iri mai kyau.

Har ilya yau, hukumar ta Mdd ta tabbatar da cewa akwai kuma wasu mutanen miliyan 12 dake bukatar agajin abin ci cikin gaggawa a wasu kasashe a kudancin nahiyar Africa.

A gaba daya dai a cewar hukumar ta Mdd, akwai bukatar tsabar kudi har dalar Amurka miliyan 240 don ci gaba da gudanar da wannan gagarumin aikin na ceto rayuwar miliyoyin mutane a nahiyar ta Africa da yunwa kewa barazana.

Ya zuwa yanzu dai a cewar hukumar, an samu tallafin kudade da yawan su ya tasamma dalar Amurka miliyan 18 da digo biyar daga cikin adadi na sama da take bukata.

Bisa hakan a cewar, mataimakin shugaban hukumar ta bada tallafin abincin ta Mdd, wato Jean Jacques Graisse, akwai bukatar kasashen da suka yi alkawari na taimakawa dasu kokarta don cika alkawarurrukan da suka yi, yin hakan a cewar babban jami´in ka iya taimakawa wajen ci gaba da gudanar da aiyukan bada tallafin ba tare da fuskantar wata matsala ba.

A waje daya kuma, babban jami´in hukumar ta Mdd yayi gargadin cewa ci gaba da tashe tashen hankula a gabashin kasar Chadi ka iya kawo tsaiko ga aiyukan hukumar na bawa yan gudun hijira daga kasar Sudan dake da matsugunan su a kusa da gurin,tallafin abin ci, wanda aka kiyasta yawan su ya kai a kalla dubu dari biyu.