1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajen India Natwar Singh ya yi murabus

November 8, 2005
https://p.dw.com/p/BvM6

Ministan harkokin wajen India Natwar Singh ya sauka daga mukamin sa, a sakamakon wani rahoto da ya baiyana cewa ya amfana daga tabargazar shirin nan na sayar da mai domin sayowa alúmar Iraqi abinci. A yanzu maáikatar harkokin wajen zata kasance karkashin kulawar P/M Indian Manmohan Singh. Sai dai kuma an baiyana cewa Natwar Singh zai cigaba da kasancewa a cikin majalisar zartarwar kasar har ya zuwa lokacin da zaá kammala bincike. A waje guda kuma hukumomi a nan Jamus sun fara binciken wani tsohon maáikacin kamfanin motoci na DaimlerChrysler a game da wata almundahana ta sayarwa da kasar Iraqi motoci bayan sanya mata takunkumi daga majalisar dinkin duniya. An zargi jamiín kamfanin da bada toshiyar baki tare da samun takardar safarar motocin ba bisa kaída ba