1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan Harkokin Wajen Jamus A Kasar Indiya

July 14, 2004

Maganar neman kujera ta dindindin da kasashen Jamus da Indiya ke yi a kwamitin sulhu na MDD ita ce ta fi daukar hankali a shawarwarin da ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya gudanar tare da wakilan gwamnatin kasar Indiya

https://p.dw.com/p/Bvi9
Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer lokacin da yake ganawa da P/M kasar Indiya Manmohan Singh
Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer lokacin da yake ganawa da P/M kasar Indiya Manmohan SinghHoto: AP

Dukkan kasashen na Jamus da Indiya na gwagwarmayar neman dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhu na MDD da kuma neman ganin an yi wa tsare-tsaren ayyukan majalisar da kafofinta kwaskwarima. Dukkan kasashen biyu, kamar yadda aka ji daga Joschka Fischer da takwaransa na kasar Indiya Natwar Singh, na neman kujera ta dindindin a duk lokacin da aka tsayar da shawarar kara yawan wakilan kwamitin sulhun MDD. Akwai bukatar kawo canji ga kafofin majalisar domin dacewa da sabon yanayin da aka shiga a wannan karni na 21 da muke ciki, inda kasashe masu tasowa ke da hakkin samun kujera ta dindindin daidai da kasashe masu ci gaban masana’antu, wadanda ke ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiyar duniya irinsu Jamus. Irin wannan canjin shi ne zai ba wa ayyukan majalisar karin tasiri bisa manufa. A ziyararsa ta kwanaki goma ga kasashen Asiya, ministan harkokin wajen na Jamus dake samun rakiyar gaggan wakilan ‚yan kasuwa, zai mayar da hankali ne wajen neman goyan baya ga fafutukar da kasar ke yi na neman dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhu na MDD. A baya ga kasar Indiya, Fischer zai yi balaguron kasashen China da Bangladesh da Sri Lanka da kuma Pakistan domin tattaunawa a game da hanyoyin kyautata dangantakar tattalin arziki ta kasa da kasa. Ministan harkokin wajen na Jamus shi ne na farko daga jerin ministocin harkokin wajen kasashen yammaci da ya kai ziyarar ban girma ga P/M Manmohan Singh da ministan harkokin wajen Indiya Natwar Singh. Babu dai wani banbancin ra’ayi na a zo a gani da aka samu a shawarwarin da Fischer ya gudanar da jami’an sabuwar gwamnatin kasar ta Indiya. A lokacin da yake bayani Fischer cewa yayi:

Bisa ga ra’ayinmu tuni tsarin MDD ya zama tsofon yayi, wanda yayi daura da siyasar duniya a karni na 21 kuma wajibi ne a yi wa majalisar gyaran fuska. Kasashen Jamus da Indiya na bukatar samun dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu na MDDr kuma zasu taimaka wa juna domin cimma wannan manufa.

Fischer dai bai yi wata-wata ba wajen bayyana goyan bayansa ga kusantar junan da ake samu sannu a hankali tsakanin Indiya da Pakistan ko da yake bai fito fili ya kalubalanci matakin da Indiya ta gabatar na shigence lardin Kashmir ba kamar yadda Isra’ila ke neman shigence yankunan Palasdinawa masu ikon cin gashin kansu. A maimakon haka ministan harkokin wajen na Jamus nuni yayi da cewar wajibi ne kasar ta Indiya tayi bakin kokarinta domin karya alkadarin ‚yan ta’addanta a cikin gida. Da zarar al’amura sun daidaita za a wayi gari wannan shingen ba ya da wani tasiri. Daga kasar ta Indiya Fischer zai zarce zuwa Beijin fadar mulkin kasar China.