1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajen Jamus ya ce gamayyar ƙasa da ƙasa ta sami nasara wajen yaƙi da ta’addanci.

October 26, 2006
https://p.dw.com/p/BueK

Ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya ce yaƙi da ta’addancin da gamayyar ƙasa da ƙasa ta ƙaddamar don tabbatad da zaman lafiya a duniya ya sami gagarumar nasara. Steinemeier ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi yau gaban majalisar dokokin Jamus ta Bundestag a birnin Berlin, wadda ke muhawara kan batun tsawaita wa’adin dakarun Jamus a fafutukar ta yaƙi da ta’addanci, da aka yi wa laƙabin „Enduring Freedom“.

Ministan tsaro na tarayyar Jamus Franz-Josef Jung, shi ma ya yi wa taron majalisar jawabi, inda ya ƙarfafa cewa, wajibi ne a huskanci duk wata barazanar ta’addanci da za ta kunno kai ko ina ne kuma a duniya. Ƙalubalantar barazana a inda ta kunno kai, ita ce hanya mafi inganci wajen kare al’umman Jamus, inji ministan. Sabili da haka ne dai ya yi kira ga majalisar da ta amince da tsawaita wa’adin dakarun. Franz-Josef Jung ya ƙara da cewa:-

„Ina mai ra’ayin cewa, wajibi ne gare mu da mu tsawaita wa’adin dakarun har tsawon watanni 12 masu zuwa, saboda idan muka huskanci rikice-rikice da tashe-tashen hankulla a cikin lokaci kuma a inda suke da asali, hakan zai kasance mataki mafi inganci wajen kare al’umman ƙasarmu.“