1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajen Jamus ya kammala rangadin kwanaki 10 a nahiyar Asiya.

Mohammad Nasiru AwalJuly 23, 2004
https://p.dw.com/p/Bvho
Lokacin da Fischer ya isa kasar Pakistan, mataki na karshe a rangadin da ya kaiwa kasashen Asiya
Lokacin da Fischer ya isa kasar Pakistan, mataki na karshe a rangadin da ya kaiwa kasashen AsiyaHoto: AP

Ko tantama babu, jawabin da ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya yi a birnin Peking ya burge jama´a, musamman masu fafatukar kare hakkin dan Adam. To sai dai kafofin yada labarun China wadanda ke hannun hukuma, sun ki watsa kalaman sukar manufofin hakkin dan Adam na gwamnatin birnin Peking da mista Fischer yayi. Hakazalika kalaman na shi ba zasu sanya cikin dare daya mahukuntan China sun rufe gidajen kurkuku ko kuma su ba jama´a damar fadar albarkacin bakinsu ba. Shi dai Joschka Fischer ba kamar shugaban gwamnatin Jamus ba, ya fito fili ya yi magana game da hakkin dan Adam da kuma halin da ake ciki a Taiwan da Tibet. Hakan dai ya nunar a fili cewar Jamus ba ta aiwatar da manufarta ta ketare don kawai ta dadadawa abokannen huldar cinikinta ba, a´a da akwai wasu dokoki da ka´idoji da ta ke bi.

Manufofin ketare na wannan kasar na goyon bayan mulki na demukiradiyya, kare hakkin dan Adam, warware rikice-rikice cikin lumana, taimakon jin kai da kuma ba da gudummawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya a duniya, kamar wanda take yi yanzu haka a kasar Afghanistan. Irin wadannan manufofin ne kuwa ita ma MDD ta ke bi. A saboda haka ba abin mamaki ba ne da gwamnatin birnin Berlin, wadda ta ke mastayi na uku a jerin kasashen da suka fi ba MDD taimakon kudi kuma har wayau ita ce ta biyu a wajen ba da yawan sojoji dake aiki karkashin lemar MDD ke kara matsa kaimi don samun kujerar dindindin a kwamitin sulhu ko kuma a hada a bata wannan kujera tare da KTT. To sai dai hakan ba zai tabbata ba a cikin wani gajeren lokaci nan gaba, musamman idan aka yi la´akari da cewa Fischer ba cimma wata nasara ta ku zo ku gani game da wannan batu a rangadin na nahiyar Asiya ba.

Alal misali kasar Indiya wadda ita ma ke neman dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhu, ta ce zata goyi bayan Jamus ne idan Jamus din ta goya mata baya. Yayin da Pakistan da kuma sauran kasashen da Fischer ya ziyarta ba su ba da wani tabbaci ba.

A halin da ake ciki nahiyar Asiya na jan hankalin kasashen yamma masu karfin tattalin arziki, musamman saboda bunkasar tattalin arziki da ake samu a wannan nahiya. To amma a lokaci daya kuma bai kamata a yi watsi da rikice-rikice da rashin tsaro da ake fama da su a wannan nahiya ba. Ga kasashen Asiya na Jamus na taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arziki, amma idan aka zo batun tsaro Jamus ba ta wani katabus.

Ko da yake wannan ziyara daya kwal da ministan harkokin wajen ya kai nahiyar Asiya ba zata canza kome ba, to amma rashin basira ne a ce ziyarar ba ta yi nasara ba.