1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajen Jamus yana Beirut

December 2, 2006
https://p.dw.com/p/BuZN

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeir,ya isa birnin Beirut ,domin tattaunawa da prime ministan Lebanon Fouad Siniora.Kafin isarsa fadar gwamnatin kasar,ya yada zango a zirin Gaza ,inda ya jaddada bukatar sake farfado da daftarin samar da zaman lafiyan yankin gabas ta tsakiya.Bayan ganawarsa da shugaba Mahmoud Abbas,Steinmeire yace ,yayi imanin cewa ,zaa shawo kann rikicin dake addaban yankin palasdinawa.Ya kuma sake jaddada manufarsa wajen farfado da tattaunawar bangarori 4 akan yankin daya hadar da Amurka da Rasha da Kungiyar EU da mdd.