1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan Kwadago na Britania ya yi murabus

November 2, 2005
https://p.dw.com/p/BvMr

Ministan kwadago na kasar Britania David Blunkett yayi murabus daga mukamin sa a sahiyar yau laraba.

Masharahanta na nuni da cewa wannan murabus da wani na hannun damar Tony Blair ya yi zai kara saka Praministan a cikin wani saban yanayi da karya garfin gwiwa, bayan zargi da ya ke samu daga masu adawa da siyasar Britania a kasar Iraki.

A daya wajen kuma, kungiyar kare hakokin bani Adama ta Amnisty Internationl ta soki gwamnatinTony Blair da cin zarafin bani adama, ta hanyar sabin dokokin da ta bullo da su a yaki da ta´adanci.

Wannan dokoki inji kungiyar sun sabawa dokokin kariyar hakokin jama´a na kasa da kasa.

Britania, na daukar su domindadadawa Amurika, da ta shiga yaki ta ta´adanci tun bayan hare haren 11 ga watan Satumber na shekara ta 2001.