1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan tattalin arziki na ƙasar Maroko na ziyarar Jamus don neman masu zuba jari a ƙasarsa.

November 17, 2006
https://p.dw.com/p/BubU

Yayin da ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ke rangadi a ƙasashen Larabawa na arewacin Afirka, inda a yau ne ya da zango a ƙasar Maroko, ministan harkokin tattalin arziki na wannan ƙasa, Rachid Talbi El Alami, ya iso nan Jamus don neman masu zuba jari a ƙasarsa.. Da yake yi wa maneman labarai jawabi yau a birnin Berlin, minstan ya bayyana cewa, ƙasar Maroko na samu ci gaba sosai a fannin tattalin arzikinta. Ya ce a shekarar nan kawai ƙiyasi na nuna cewa, ƙasarsa za ta sami bunƙasar tattalin arziki na kashi 8 cikin ɗari. Amma duk da haka, Marokon na huskantar wasu mattsaloli. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Muna ƙoƙarin kasancewa kan gaba a tserereniyar tattalin arzikin yankinmu. Kuma mu ne a kan gaban. Matsalar da muke huskanta a halin yanzu kawai ita ce rashin ƙwararrun ma’aikata. Sabili da haka, mun gabatar da wani sabon shiri na gaggawa, don mu iya horad da injiniyoyi dubu 10 a ko wace shekara.“