Ministar harkokin wajen Tanzania ta zama mataimakiyar sakataren MDD
January 5, 2007Talla
Babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya nada ministar harkokin wajen Tanzania Asha-Rose Migiro a mukamin mataimakiyar sa. Wannan tamkar cika alkawarin da ya yi ne na nada mace don ta rike wannan mukami na biyu mafi daraja a MDD. A lokacin bukin nadin ta Ban Ki Moon ya bayyana Rose Migiro a matsayin wata shugaba da ake girmamawa wadda ta san makaman aiki kuma ta yi fice a kasashe masu tasowa. Ban ya ce zai mayar da hukumomi da dama na sakatariyar MDD a karkashin ofishin mataimakiyar ta sa. Ban tsohon ministan harkokin wajen KTK shi ne sakatare janar na MDD na 8 bayan ya gaji Kofi Annan dan kasar Ghana a ranar litinin da ta gabata.