1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministar tsaron Faransa ta yi murabus

Mouhamadou Awal Balarabe
June 20, 2017

Ministoci biyu na kasar ciki har da ministar tsaro Sylvie Goulard sun yi musarabus sakamakon wata badakalar ayyukan boge da ake zarginsu da aikatawa.

https://p.dw.com/p/2f47R
Mali  Sylvie Goulard Verteidigungsministerin Frankreich
Hoto: Getty Images/AFP/C. Tesson

Ministoci biyu na kasar sun yi musarabus sakamakon wata badakalar ayyukan boge da ta kunno kai a Jam'iyyar MoDem mai kawance da ta shugaba Emmanuel Macron. Ba zato ba tsammani ne ministar tsaro Sylvie Goulard ta ce ba zata ci gaba da rike mukamin gwamnati ba, domin zata yi kokarin wanke kanta daga zargin da ake mata.

Dama Richard Ferrand da ke da kusanci da shugaban kasa, wanda shi ma yake fuskantar tuhuma bisa zargin barnatar da kudaden gwamnati tun kafin ya zama dan majalisa, ya amince ya sauka daga mukaminsa. Sai dai ganbaren gwamnatin Faransa ya bayyana cewar zai tsayar da shi takarar kujerar shugaban masu rinjaye a majalisar dokoki.

Shugaba Macron ya yi alkawarin dawo da martabar gwamnati a idon Faransa da Kungiyar Tarayyar Turai ta hanyar raba gari da duk wani babban jami'in da za a tuhuma da aikata ba daidai ba. Yanzu maka dai gwamnatinsa na shirin shigar da daftarin doka kan haramta wa 'yan siyasa yin gaban kansu a fannin kashe dukiyar kasa.