1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin harkokin wajen Ƙungiyar Haɗin Kan Turai na taro a birnin Brussels kan batun shigar Turkiyya a ƙungiyar.

December 11, 2006
https://p.dw.com/p/BuYM

Ministocin harkokin wajen Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, sun fara wani taro yau a birnin Brussels, don tattauna yadda za su ci gaba da batun neman shiga ƙungiyar da Turkiyya ke yi. Amma ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya ce akwai wani babban giɓi na bambancin ra’ayoyi tsakanin ƙasashe mambobin ƙungiyar dangane da wannan batun, abin da zai ƙara dagula al’amura wajen cim ma daidaito kan shawarar da taron zai yannke. Kawunan ƙasashen EUn sun rarrabu ne game da irin matakan da ƙungiyar za ta ɗauka kan birnin Ankara, saboda ƙin da gwamnatin Turkiyyan ta yi na buɗe wa ƙasar Cyprus, tashoshin jiragen ruwa da kuma filayen jiragen samanta.

Hukumar ƙungiyar EUn dai ta ba da shawarar soke duk tattaunawa da Turkiyyan a kan batun zamowarta mambar ƙungiyar, har tsawon wani lokaci na wucin gadi. A taron ƙoli na shugabannin gwamnatocin ƙasashen ƙungiyar, da za a gudanar a birnin Brussels a ran alhamis da juma’a mai zuwa, batun hulɗa tsakanin EUn da Turkiyya, zai kasance ɗaya daga cikin muhimman ajandar taron.