1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin Turai da na Afrika na taro a game da matsalolin bakin haure a birnin Raba

July 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bur2

A birnin Rabat na kasar marroko, an buɗa taron ministoci da su ka zo daga ƙasashe 30 na Afrika, da kuma 27 daga nahiyar turai, dukan su masu fuskantar matalolin baƙin haure.

Mahalarta wannan taro, za su masanyar ra´ayoyi a game da matsalolin baƙin haure, da ke kwarara daga Afrika zuwa turai ,da kuma haɗɗarruruka iri iri, da ke tattare da wannnan gudun hijira.

A ƙarshen wannan taro, a na sa ran hiddo wata sanarwa ta haɗin gwiwa tsakanin turai da Amurika, wadda zata magance matsalolin baƙin haure, da ke shirin zama gagarabadau.

Shugaban ƙasar France Jacques Chirac, ya aika jawabi a bikin bude taron, inda ya bayyana aniyar France, ta yaƙar al´ammuran baƙin haure ba tare da sassauci ba,

to saidai, kuma ya tabatar da cewa France zata wannan aiki ta hanyar kare haƙƙoƙin jama´a.