1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Misalin shekaru 15 da suka wuce aka fatattaki Iraki daga Kuwait

January 17, 2006

A daidai ranar 17 ga watan janairun 1991 kasashen taron dangi suka gabatar da matakin korar Iraki daga Kuwait

https://p.dw.com/p/Bu2N
Gobara a rijiyoyin man Kuwait 1991
Gobara a rijiyoyin man Kuwait 1991Hoto: AP

A daidai ranar biyu ga watan agusta na shekarar 1990 ne tsofon shugaban kasar Iraki Saddam hussein ya tura sojojinsa domin mamayar kasar Kuwait, wacce makonni kalilan bayan haka yayi ikirarin cewar wai wani lardi ne na kasar Iraki. Ainifin dalilin wannan mataki da Saddam Hussein ya dauka kuwa shi ne dimbim bashi na kwatankwacin Euro miliyan dubu 40 da suka taru kan kasar Iraki sakamakon yakinta da Iran. Tattalin arzikin kasar ya gurgunce saboda shugaba Saddam Hussein yayi amfani da kudaden shiga da Iraki ke samu daga cinikin mai wajen sayen makamai. A wancan lokaci kuwa kasashen Kuwat da hadaddiyar daular Larabawa su ne gaggan masu ba wa kasar Iraki lamuni. Saddam Hussein ya nema daga gare su da su rage yawan mai da suke haka ta yadda Iraki zata cike gibin da zai samu a kasuwannin duniya domin samun karin kudaden shiga. Kazalika yayi kira ga kasashen na mashigin tekun pasha da su yafe wa kasarsa dimbim bashin da suke binta. Amma kasashen na Kuwait da hadaddiyar daular Larabawa sun yi ko oho da wannan kira. A maimakon haka ma sai suka kara bunkasa yawan mai da suke haka yadda Iraki ta tashi a tutar babu. Ganin haka shugaba Saddam Hussein bai yi wata-wata ba da zargin Kuwait da laifin satar mai kuma yayi imanin cewar mamayar Kuwait ita ce kawai zata taimaka kasar Iraki ta fita daga mawuyacin hali na tattalin arzikin da take ciki, kazalika ta haka ne zai bi gurabun tsofon shugaban kasar Masar Gamal Abdannassir domin zama jagora ga illahirin Larabawa. Amma ga alamu tsofon shugaban na Iraki yayi sara ne ba tare da duban bakin gatari ba. Domin kuwa kasa kamar Amurka ba zata yarda da canjin angizo a wannan yanki ba saboda muhimmancinsa ta fuskar tsaro da tattalin arziki. Shi kuma kwamitin sulhu na MDD tun a ranar ta biyu ga watan agustan 1990 yayi kira ga Iraki da ta janye sojojinta daga Kuwait nan take kuma ba tare da gindaya wani sharadi ba. Kwanaki hudu bayan haka kwamitin na sulhu ya kakaba wa Iraki takunkumin karya tattalin arzikin kasa da haramcin ma’amallar soja da ita. A nasa bangaren tsofon shugaban Amurka Goerge Bush Senior ya tura sojoji dubu 400 domin ba da kariya ga kasar Saudiyya. Ba a kuma dade ba aka samu hadin kai kasashe domin yi wa Iraki taron dangi, abun kuwa da ya hada har da kasashen Larabawa, in banda kasar Jordan, wadda ta dade tana fuskantar barazana daga Iraki. Ganin mawuyacin halin da ya samu kansa a ciki shugaba Saddam Hussein ya fara kame-kame da ikirarin magana da yawun al’umar Palasdinu, sannan ya kira taron Yankin Gabas ta Tsakiya domin tattauna maganar janyewar daga Kuwait. Bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi, a daidai ranar 17 ga watan janairun shekarar 1991 shugaban Amurka George Bush senior ya ba da umarnin kai wa Iraki farmaki. A cikin kiftawa da Bisimillah aka yi kaca-kaca da kafofin soja da masana’antun Iraki. Kuma a ranar 28 ga watan fabarairun shekarar ta 1991 Saddam Hussein ya ba da kai bori ya hau yana mai rattaba hannu akan yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma amincewa da wasu kudurori goma sha biyu na MDD. Kuma da yake tabarmar kunya da hauka ake nade ta, sojojin Irakin kafin su janye daga Kuwait sai da suka cunna wa rijiyoyin manta guda 700 wuta.