1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mista Annan ya yi kira da a taimakawa lardin Darfur

May 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuzS

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi kira da a ba da gagarumin taimako ga lardin Darfur mai fama da rikici a yammacin Sudan. Wannan kiran ya zo ne bayan da babbar kungiyar ´yan tawayen lardin da kuma gwamnatin Sudan suka sanya hannu akan wata yarjejeniyar samar da zaman lafiya a wani yunkurin kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru 3 ana yi a lardin na Darfur. Bayan an shafe kwanaki da dama ana tattaunawa a Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya, a jiya juma´a kungiyar Sudan Liberation Army da gwamnatin Sudan sun amince da wani shirin wanzar da zaman lafiya wanda kungiyar tarayyar Afirka ta dauki nauyin tsara shi. Wasu rahotannin da ba´a tabbatar da su ba sun ce daya daga cikin kungiyoyin ´yan tawaye biyun da suka yi watsi da yarjejeniyar, yanzu ta sanya hannu akan wannan yarjejeniya ta zaman lafiya. To amma har yanzu daya kungiyar na ci-gaba da nuna adawa, abin da ya sa ake nuna shakku game da dorewar yarjejeniyar. Rikicin na yankin Darfur dai ya yayi sanadyiar rayukan dubun dubatan mutane yayin da sama da miliyan biyu kuma suka tsare daga gidajensu.