1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mnangagwa ya nada sabbin ministoci

Abdul-raheem Hassan
December 1, 2017

Sabon shugaban kasar Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa ya bayyana sunayen mutanen dai zai yi aiki da su a gwamnatinsa a matsayin ministoci ciki kuwa har da sojoji da wasu mukarabban tsohon shugaba Robert Mugabe.

https://p.dw.com/p/2oaCT
Emmerson Mnangagwa Politiker aus Simbabwe
Hoto: Getty Images/AFP/A. Joe

Daga cikin ministocin da Mr. Mnangagwa ya nada akwai Patrick Chinamasa wanda zai jagoranci ma'aikatar kudi yayin da Major Janar Sibusiso Mayo ke a mastayin minsitan harkokin kasashen waje, shi kuwa Air Marshal Perrance Shiri a matsayin minista na kasa. Mnangagwa ya kuma maido da wasu mukarraban gwamnatin tsohon shugaban Zimbabuwe Robert Mugabe a cikin sauran mukaman gwamnati da ya nada, abin da masharhanta ke ganin ka iya haifar da kakkausar suka daga wasu 'yan kasar. A yanzu dai sabon shugaban Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa na cikin kalubalen sauya lamuran kasar musamman farfado da tattali arziki da haifar da karancin kudaden ketare da ya yi sanadiyar jefa kasar cikin mawuyacin hali.