1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mohamed El baradei ya samu lambar yabo a Jamus

March 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3z

Shugaban hukumar Majalisar Ɗinki Dunia mai yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea, Mohamed El Baradei, ya kawo ziyara a ƙasar Jamus, inda a yau, ya karɓi wata lambar yabo, daga ƙungiyar ƙurrarun likitocin haƙora ta nan Jamus.

An yi bukin bada wannan lambar yabo, a birnin Karslruhe, dake kudu maso yammacin Jamus.

Ƙurrarun likitocin haƙora na Jamus, na bada wannan lamba mai taken” baki buɗe” a ko wace shekara, ga ɗan siyasar da yayi fice, ta fannin tsage gaskiya, da nuna adalci a cikin ayyukan sa.

A yayin da ya ke bayani, bayan kammalla shagulgullan, Mohamed El baradei ,ya buƙaci a gudanar da kwaskwarima, ga komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.

Kazalika, ƙasashen dunia sun samu haɗin kai, ta fanning hana yaɗuwar makaman ƙare dangi.

Ranar litinin idan Allah ya kai mu, El Baradei, zai gana da shugabar gwamnatin Jamus Angeller Merkel, da ministan harakokin waje, Frank walter Steinmeir, inda za su masanyar ra´ayoyi, a game da rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran.