1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Montenegro ta ɓalle daga Serbia

May 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bux8

Hukumar zabe, a Montenegro, ta bayyana sakamakon zaɓen raba gardama, da aka gudanar ranar lahadi da ta wuce, a yankin , domin ɓallewar, Montegro daga Serbia.

Sakamakon zaɓen ya ce kashi 55 na ƙuri´un da aka kaɗa, sun amince da wannan mataki, tare da girka ƙasar Montenegro mai cikkaken yanci.

Nan gaba a yau ne, shugaban ƙasar Serbia, Boris Tadic, zai kiri taron manema labarai, domin bayana matsayin sa, a game da matakin ɓallewa, da al´umomin yankin Montegro su ka ɗauka.