1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Motocin yaki 105 sun isa kardin Darfur

Zainab A MohammadNovember 18, 2005
https://p.dw.com/p/Bu7q

SUDAN

A yau ne manyan motocin yaki suka fara isa lardin darfur dake kasar sudan,batu da jamiaai sukace yunkurin kungiyar gamayyar Afrika na karfafa matakan tsaro a wannan yanki dake fama da rikici a Sudan.

Wadannan Motocin yaki dai sun sauka ne a garin el-Fasher ,inda sabon fada ya barke tsakanin yan tawaye da mayakan larabawa,tun amakon daya gabata,wanda ya zuwa yanzu mutane 85 suka rasa rayukansu,ayayinda wasu dubu 10suka tsere daga gidajensu.

Jakada na musamman na Afrika wa yankin kuma Prime ministan Canada ,Bob Fowler ya fadawa kamfanin dillancin labaru na reuters cewa ,bayyanan wadannan dakarun zai taimaka wajen kwantar da wannan sabon rikici daya barke.Canada dai ita ta sayi wadannan motocin yaki 105,wadanda yau suka isa darfur,bayan watanni na cece kuce da gwamnatin khartum.

Premien Canada yace hakan zai taimaka wajen kare yarjejeniyar zaman lafiya da ake kokarin cimma ,tare da bawa ayarin dakarun kiyaye zaman lafiyan AU,daman gudanar ayyukansu.

Akwai kimanin dakarun kiyaye zaman lafiya nas Afrika 6,000,dake cigaba da kasancewa a wannan lardi na darfur,wadanda suka fuskanci barazanar hare hare na kwanton bauna,wanda ya ritsa da wasu a watan daya gabata.