1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mr Anan da Mr Olmert sun gana a Jerusselem

August 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bul9

Faraministan Israela Ehud Olmert, yace yana fatan yarjejeniyar sulhun da aka cimma tsakanin su da kungiyyar Hizboulla, zata zama kashin bayan kyautata dangantaka, a tsakanin Israela da kasar Libanon.

Faraministan na Israela ya fadi hakan ne a lokacin taron manema labarai daya gudanar tare da Mr Kofi Anan sakataren Mdd , a birnin Jerusselem.

A nasa bangaren, Mr Anan cewa yayi Mdd zata yi duk iya bakin kokarin ta nan bada dadewa ba wajen fadada tawagar dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar a kasar ta Libanon.

Ana dai sa ran kara yawan dakarun sojin ne izuwa a kalla dubu biyar inji Mr Anan cikin yan kwanaki kadan masu zuwa.

Har ilya yau Mr Anan ya kuma jaddada muhimmacin kawo karshen kawanyar da Israela tayiwa Libanon.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa dukkannin shugabannin biyu , wato Mr Anan da Mr Olmert sun jaddada goyon bayan su, na ganin an sako sojin Israelan nan biyu da kungiyyar Hizboullah ke tsare dasu ba tare da gindaya wasu sharudda ba.