1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mr Egeland na shirin kammala ziyarar kwanaki uku a Icoast

Ibrahim SaniFebruary 17, 2006

Mdd ta bukaci a hukunta wadanda suka tashi zaune tsaye a Icoast a watan janairun daya gabata

https://p.dw.com/p/Bu1b

Ya zuwa yanzu dai kafafen yada labarau sun rawaito Mr Egeland na fadin cewa, Mdd zata mayar da jami´an ta masu bayar da agajin gaggawa da dakarun kiyaye zaman lafiya izuwa yammacin kasar ne kawai bisa cika wasu sharruda.

Daga cikin wadannan sharruda kuwa a cewar Mr Egeland, akwai bukatar tabbatar da tsaron lafiyar ma´aikatan bayar da agajin a hannu daya kuma da ladaftar da wadanda suka haddasa fitinar nan data haifar da zaune tsaye a birnin Abijan da kuma wasu birane a kasar a watan janairun daya gabata.

Har ilya yau Mr Egeland ya bukaci gwamnatin kasar ta Ivory coast data dauki kwararan matakai na cafkewa tare da ladaftar da duk wani mutum da yayi kokarin tashin zaune tsaye a cikin kasar a nan gaba.

Mr Egeland wanda ya fadi hakan bayan wata tattaunawa da yayi da jamian gwamnatin kasar a yau ya kara da cewa daukar wannan mataki daga bangaren gwamnatin kasar itace hanya da zata karawa kungiyoyin sa kai da jami´an bayar da agaji kwarin giwar ci gaba da gudanar da aikin su ba tare da wata fargaba ba.

Idan dai za´a iya tunawa wannan zanga zanga data faru a watan na Janairu, bayanai sun nunar da cewa matasa ne magoya bayan shugaba Lauret Gabgbo suka gudanar da ita, wanda a lokacin suka bukaci ficewar jami´an Mdd daga cikin kasar baki daya, bisa hujjar cewa suna yi musu katsalandan a harkokin cikin gida na kasar.

Bisa kuwa irin yadda masu zanga zangar suka lalata kayayyakin hukumar ta Mdd a kasar, tuni babban magatakardar majalisar, wato Mr Kofi Anan ya aikewa da shugaba Lauret Gabgbo takardar dar biyan diyya na kayayyakin da aka lalata, da yawan su ya tasamma dalar amurka miliyan uku da digo shidda.

Rahotanni dai sun nunar da cewa daya daga cikin shugabannin matasan, wato Chief Denis Naho daya kalubalanci zaman jami´an Mdd a cikin kasar ta Ivory Coast, a yanzu haka ya daukaka kira da cewa su dawo bakin aikin su a yammacin kasar komai ya dai dai ta, domin kin dawowar su ka iya haifar da wani yanayi na tsaka mai wuya ga mazauna yankin.

Mr Egeland, wanda a yau yake kammala wannan ziyara ta kwanaki uku, a jiya alhamis ya ziyar ci garin Guiglo inda aka kaiwa kaiwa jami´an mdd hari, don kalailai ce yadda yanayin rayuwar mutanen yankin yake, wanda da yawa yawan su ke bukatar tallafin gaggawa.

Kafafen yada labaru dai sun rawaito wakilan mazauna garin na Guiglo na rokon Mdd data dawo da ma´aikatan nata izuwa yankin don ci gaba da gudanar da aikin su.

Zongo Ousseni,manomi dake zaune a garin na Guiglo ya tabbatar da cewa a yanzu haka rayuwar su na cikin hatsari a sabili da rashin kyakkyawan tsaro, sannan a hannu daya babu masu tallafa musu daga hukumar bayar da tallafi ta mdd, a don haka a cewar manomin a yanzu sun zama tamkar marayu.