1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muƙaddashin Shugaban Najeriya zai kai ziyarar aiki Amirka

April 9, 2010

A karon farko tun bayan daya ƙarɓi ragamar shugabancin Najeriya, Muƙaddashin shugaban ƙasa Jonathan Goodluck zai gana da Shugaban Amirka Barack Obama

https://p.dw.com/p/Mrys
Muƙaddashin Shugaban Najeriya Jonathan Goodluck.Hoto: AP

A karon farko tun bayan daya ƙarɓi ragamar shugabancin Najeriya, Muƙaddashin shugaban ƙasa Jonathan Goodluck zai kai ziyarar aiki ƙasar Amirka. A lokacin wannan ziyara, Goodluck zai gana da Shugaba Barack Obama da nufin tattauna hulɗan dake tsakanin ƙasashen biyu. Wannan ne dai karon farko da Shugaba Obama zaiyi tozali da wani babban jami'in gwamnatin Najeriya da nufin tattauna matsalar data kunno kai tun bayan  yunƙurin tarwatsa wani jirgin saman Amirka da wani ɗan Najeriya yayi a ranar kirsimati. Ko'a wannan mako sai da Muƙaddashin shugaban Najeriyan, ya gana da Alhaji Umaru Mutallab, mahaifin matashin a Abuja. A yayinda Sakatariyar harkokin tsaron cikin gidan Amurka Janet Napolitano, itama zata kawo ziyarar aiki Najeriya a makon gobe domin tattauna batun tsaro a filayayen Jiragen saman Najeriya. Sauran batutuwan da ake sa ran shugabanin biyu zasu taɓo sun haɗa da batun gudanar da ingantaccen zaɓe a Najeriya. Tuni dai Amurka tayi kira ga shugaban Hukumar zaɓen Najeriya Mourice Iwu daya sauka daga kan muƙamin sa. 

Mawallafi: Babangida Jibril   

Edita: Yahouza Sadisou Madobi