1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mu'amula tsakanin Musulmi da Kirista a Kenya

December 28, 2016

Domin samun fahimtar juna da kuma samar da kyakyawar zamatakewa tsakanin Musulmin da Kirista,an aiwatar da shirin yin penti iri daya mai ruwan dorowa ga Masalsatai da kuma Coci a Kenya.

https://p.dw.com/p/2UxaD
Afrika Kenia - Gelb gestrichene Kirchen als Symbol des Friedens
Hoto: picture-alliance/AA/R. Canik

Wannan kiran Sallah ke'nan a wani Masallacin da ke a wata unguwar da ke a wajen baban birnin Kenya watau Nairobi inda jama'a suka tataru domin yin Sallah, wannan masalaci da ke a Kibera shi ne mafi girma a Kenya,inda matasa suka taru suna yin aiki tare da sauran 'yan uwansu Kirista.Vincent Ayacko kirista ne kuma yana daya daga cikin matasan da suke yin aikin:''Musulmi da Kirista su kan hadu suna yi aikin penti na Masallatai da Coci tare abin gwanin sha'awa.''

Kamar yadda aka yi wa Masallacin penti mai ruwan dorowa haka ita ma Cocin da ke cikin unguwar aka yi mata penti wacce ba ta wucce nisan mita 100 tsakanita da Masallacin ba.