1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara gabanin zaben shugaban kasar Ghana

November 30, 2016

A yayin da ya rage kwanaki kalilan a gudanar babban zaben shugaban kasa a Ghana, jama’a na nuna cewar yanayin tabarbarewar tattalin arziki da matsalar makashi da sauransu ne muhimman abubuwan sauraro daga 'yan takara

https://p.dw.com/p/2TXOa
Bildergalerie Präsidentenpaläste Ghana
Hoto: picture-alliance/dpa/UPPA/Photoshot


A cikin shekarun da suka gabata, jama’ar Ghana da dama ne ke dogara da kada kuri’unsu a bisa hujjojin da ba sa rasa nasaba da kudurorin dan takara, surarsa, addininsa, kabilarsa da dai sauransu. Amma dai a wannan karon duk wadannan basu da wani tasiri a yayin da aka fi mayar da hankali a kan halin rayuwa da yanayin tattalin arziki. Kuma a kan wannan batu dai matasa da dama ne ke nuna mabambamtan ra’ayoyinsu.

Sakamakon kiyasin da Cibiyar bayar da shawarwari a kan kudurorin bunkasa tattalin arzikin kasa na Ghana, wato IEA ta yi tsakanin watannin Yuni da Yulin shekara ta 2014 a fadin kasar, ya nuna cewa kaso 77 cikin 100 na jama’a, suna duba ma’aunin ilimi ne da kuma gogewar dan takara, an samu kaso 59.1% da suka nuna ra’ayin jam’iyya, kana wasu bangarori na rayuwa kama daga zamantakewa, kabila, addini da dai sauransu.

Sai dai kuma kusan kaso 80 cikin 100 na daukacin jama’a ne, suka bayyana cewar babbar madogarar hujjarsu ta kada kuri’a a kasar ta Ghana, sun bayyanan cewa 'yanci da fadan albarkacin baki shi ne babban abin da ya fi damunsu.