1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan amfani da hijabi a Jamus

Usman Shehu Usman
April 17, 2018

Batun amfani da hijabi da kananan yara ‘yan mata ke yi a Jamus ya janyo muhawara a kasar saboda yadda ake samun karuwar al’umar musulmi a kasar. Wasu Jamusawa dai na ganin hakan tamkar takurawa rayuwar yaran ne.

https://p.dw.com/p/2wBWx
Malaysia - Shah Alam - Kinder üben für Haji in weissen Roben
Wasu kananan yara sanye da hijabiHoto: Getty Images/AFP/M. Rasfan

Wannan batun dai na zama mai matukar sarkakayi a tsakanin wasu makarantun Jamus, yayin da muhawarar ke karuwa, haka kuma 'yan mata da kananan yara mata da ke sa hijabin ke karuwa a makakarantun kasar ta Jamus. Thomas Böhm kwararre ne a fannin hakkin 'yan makaranta, ya kuma bayyana cewa:

"Muhawara bisa karuwan karfin addinai da kuma al’umomin addinan a makarantu, a wani abin da ya shafi bambancin al'ada. Muhawarar abu ne mai kyau, to sai dai ayar tambaya ita ce shin ana iya kawo karshen lamarin? A ce wai 'yan mata ‘yan kasa da shekaru 14 kar su sa hijiabi, ina ganin ba shi ne zai iya kawo karshen muhawarar ba"

Duk da karuwar muhawarar, har yanzu dai babu wata matsaya ko doka da makarantu suka saka kan yaran da ke sa hijiabin, domin kuwa akwai wasu malaman kansu da ke musulmai ne, suna sa hijabi kuma ba a haramta musu, domin a kasar Jamus doka ta yarda kowa ya bi addinin da ya ga dama.

A yanzu dai yara musulmai sai karuwa suke yi a kasar Jamus, inda wasu makarantu ake samu cikin ajin, kashi 70 zuwa 80 cikin 100 musulmai ne, don haka babu shakka batun sauyin al'adu na kan turbar sauya al'amura na rayuwa a kasar ta Jamus.