1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan takaita motocin diesel a Jamus

Suleiman Babayo
August 2, 2017

Kamfanonin kera motoci na Jamus sun amince za su inganta yanayin motoci miliyan biyar da sabuwar fasahar rage hayaki mai gurbata muhalli a manyan biranen kasar.

https://p.dw.com/p/2hZEQ
Deutschland Dieselgipfel in Berlin
Zaman taron hukumomin Jamus da shugabannin kamfanonin kera motoci a birnin Berlin.Hoto: picture-alliance/dpa/A. Schmidt

Alkaluman motocin miliyan biyar da jagororin kamfanonin suka amince da daukar mataki kansu, sun shafi motoci ne masu amfani da makamashin diesel, kuma manufar yin hakan shi ne na rage iskar da ke yi wa muhalli lahani da kashi 25 zuwa 30 cikin dari.Ganawar ta wannan Laraba ta zo ne dai dai lokacin da jami'ai da kamfanonin suka fuskanci alamun tsauraran matakan haramci kan tsofaffin nau'ukan motocin na diesel a wasu manyan garuruwan Jamus, sai kuma uwa-uba ayar tambayar da ke a kan ci gaba da amfani da fasahar a shekaru masu zuwa.

Deutschland Dieselgipfel in Berlin | Alexander Dobrindt, Verkehrsminister
Ministan suhuri na kasar Jamus Alexander Dobrindt, tare da ma'aikatansa yayin da ya iso wurin taron da gwamnati ta shirya tare da shugabannin kamfanonin motoci.Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Wata kotu da ke birnin Stuttgart na kasar ta Jamus da yake mamaye da kamfanonin kera motoci, ta bayar da mamaki bisa wani hukuncin da ake gani zai hana motocin kamfanonin Porsche da Daimler masu amfani da gas ko kuma ace diesel shiga cikin birnin nan da watanni. Hukumomin birnin Stuttgart za su tantance ko hani zai tsaya ga motocin da suka kai matakin gurbata sararin samaniya ko daukacin motoci masu amfani da gas. Haka wata kotu da ke birnin Munich ta bayar da umurnin shiri game da hana motoci masu amfani da gas.

Yunkurin takaita amfani da motocin masu aiki da gas

Symbolbild Zulassungsverbote Verbrennungsmotoren
Kokarin takaita amfani da motoci masu illa ga muhalli a JamusHoto: picture-alliance/dpa/K. D. Gabbert

Wani bincike ya nunar cewa akwai kimanin motoci milyan 35 masu aiki da gas kan titunan kasashen Turai, wadanda aka sayar cikin tsukin shekaru biyar daga shekara ta 2011 zuwa 2016, a cewar wata kungiya mai zaman kan da ke lura da sufuri mai mazauni a birnin Brussel na Beljiyam. A cewar hukumar Tarayyar Turai mai kula da muhalli, iska mai gurbata sararin samaniya ta yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 75 cikin shekara ta 2012. Kana bincike ya nuna mutane  dubu 11 da 400 ne suka hallaka a kasashen Turai saboda fitar da iskar mai gurbata sararin samaniya fiye da kima.

Yaki da dumamar yanayi a Jamus

Symbolbild Zulassungsverbote Verbrennungsmotoren
Motocin da ke fitar da hayakin da ya fice kima sun fuskanci haramci a wasu biranen JamusHoto: picture-alliance/Chromorange/Bilderbox

Kungiyar masu kera motocin na Jamus ta kuma bayyana cewa kamfanonin za su bullo da wasu dabarun kyautata cinikin irin wadannan sanfari na motoci da suke kerawa. Sai dai kuma gabanin wannan ganawar wasu masu fafutukar kare muhalli sun yi bore a gaban ofishin ma'aikatar da ke kula da sufuri da ke birnin na Berlin, suna mai nuna bukatar daukan kwararan matakai kan batun gurbata muhallin.