1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan 'yancin gudanar da addini

Suleiman Babayo/GATSeptember 15, 2016

A duniya ana kara samun mutanen da suke fuskantar musgunawa saboda addini, kamar yadda wani bincike 'yan majalisar dokokin kasashen da ya gudanar da taro a birnin Berlin na Jamus ya nunar.

https://p.dw.com/p/1K3Da
Pakistan Peschawar UNHCR Flüchtlingslager
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Sajjad

Gwamnatin Jamus ta shiga wani wadi na tsaka mai wuya kan neman hana matan Musulmai masu rufe fuska gaba daya a bainar jama'a, muhawarar da ta zafafa sakamakon shigar dubban daruruwan Musulmai kasar a matsayin 'yan gudun hijira galibi daga kasar Siriya a shekarar da ta gabata ta 2015, abin da ya kara tsoron yuwuwar samun harin ta'addanci. Shugabar gwamnati Angela Merkel ta shaida wa mahalarta taron matsayinta kan wannan batu:

"Nuna ra'ayin addini a fili da bin koyarwa da tafarkin addinin suna cikin 'yancin addini, abin da ya hada da saka kayan da mutum yake bukata. A nan akwai matsala kan hana saka wani abu gaba daya kamar rufe fuska baki daya bisa dalilan addini. Kare hakki ya hada kare da matsayin mutum na zaman daban daga saura bisa abin da yake bukata."

'Yanci addini ya shiga rudani a kasashen duniya da dama. Ko da yake kasashe 170 sun amince da kudirin Majalisar Dinkin Duniya kan kare hakkin dan Adam wanda ya kunshi 'yanci addini, ko sauya addini tare da bin abin da mutum yake so. Sai dai tuni wani bincike a Jamus ya gano cewa galibin mutane suna goyon bayan ganin haramta rufe fuska gaba daya. Ita kanta Shugabar gwamnati ta yarda akwai tarnaki da ake fuskanta, da kuma cewa hana wani yin abu na addini zai yuwu ne kawai karkashin dokokin kasa:

Frankreich Korsika Frau mit Burkini im Meer
Hoto: picture-alliance/abaca

"Ina ganin rufe fuska gaba daya da mata ke yi da burka, a matsayin tarnaki ga sajewar baki, ina da yakini kan haka. Saboda idan fuska tana rufe sanin juna da sabawa za su takaita. Haka na hana tattaunawa fiye da magana kawai. Takaita 'yancin addini zai yiwu ne kawai idan kundin tsarin mulki ya amince, ko aka saba 'yancin wani, ko kundin tsarin mulki ko kuma barazana ga 'yanci."

Ta kuma nemi ganin yadda al'ummomi daban-daban za su yi zamantakewa karkashin 'yanci da walwala. Sannan Angela Merkel ta kara jaddada muhimmanci raba addini da harkokin gwamnati:

Pakistan Peschawar UNHCR Flüchtlingslager
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Sajjad

"Raba harkokin gwamnati da addini ya hada da dama ta 'yancin addini. Abin da gwamnati za ta yi shi ne samar da yanayi da za a samu fahimta ta addini. A daya hannun muna bukatar cibiyoyi da makarantu. Malaman addini na Kirista, da Yahudawa, da limanin Musulmai ko wasu addinai suna karuwa. Iliminsu yana da tasiri kan inganci koyarwarsu."

A birnin Berlin taron na 'yan majalisun na kasashen duniya ya kuma tura wasiku ga kasashen Sudan da Myanmar kan yadda suke musguna wa tsiraru.))