1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawarar yan takarar shugabancin Faransa

May 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuMJ

Manyan yan takara dake fafatawa ta neman kujerar shugabancin ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy da Segolene Royal sun gudanar da muhawara ta kai tsaye da aka nuna ta akwatunan talabijin domin baiyana manufofin su da kuma jawo raáyin masu kaɗa ƙuriá. Yan Faransan kimanin miliyan ashirin ne suka kalli muhawarar wadda ta yi zafi tsakanin yan takara biyu Nicolas Sarkozy mai raáyin rikau da Segolene Royal ta jamíyar Gurguzu. Segolene Roayal wadda ke baya a ƙuriár jin raáyin jamaá, ta soki lamirin sarkozy wanda ya taɓa rike mukamin ministan kuɗi dana alámuran cikin gida a gwamnati mai barin gado, da cewa yana da cikin waɗanda suka haddasa koma bayan tattalin arziki da Faransa ke fuskanta wajen gaza shawo kan matsalar rashin aikin yi da gararanba a tsakanin matasa da kuma ƙaruwar munanan laifuka. A nasa ɓangaren Sarkozy ya kare matsayin sa a lokacin da yake cikin gwamnati yana mai cewa aikin saói 35 a mako illace babba ga tattalin arzikin faransa. Jamaá da dama na ganin muhawarar ita ce dama ta ƙarshe ga yan takarar su jawo raáyin masu kaɗa ƙuriá gabanin zaɓen zagaye na biyu.