1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawarori kan yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya gyara

November 12, 2012

Milyoyin 'yan Najeriya sun bayyana abubuwan da suke son ganin an gyara a tsarin mulkin ƙasar a tarurrukan da aka gudanar a mazaɓu 340 na ƙasar.

https://p.dw.com/p/16hKr
Hoto: DW

Wannan shi ne karon farko da talakan Najeriya ya samu irin wannan dama da majalisar wakilan ƙasar ta ba shi.

Tarurrukan dai sun samar da muhimmiyar dama ga talakan Najeriyar wacce ya daɗe rabonsa da jin kamshinta balle har ya ganta a aikace. Domin yanayi da ya kama hanyar kawar da hali irin na uwa da makarɓiya da 'yan siyasa da ma 'yan bokon ƙasar da suka daɗe suna amfani da gumin talakan da suna wakiltansa da muraunsa, abin da ya sanya samun sauyi a ra'ayoyin da jama'a suka bayyana.

Domin kuwa mafi yawan 'yan Najeriyar sun nuna gagarumin muradi da goyon bayan cire kariyar da gwamnonin jihohi ke da ita, wacce aka daɗe da yiwa kallo da ma zargin na ba su ikon rub da ciki a kan dukiyar al'umma, to sai dai muradun kafa 'yan sanda na jihohi bai samu goyon baya ba saboda tsoron za'a yi amfani da su don cin zarafin al'ummar ƙasar, yayin da batun sauya dokar baiwa ƙanana hukumomi 'yanci ya samu gagarumin rinjaye.

To ko me wannan ke nunawa ganin kafin wannan ba haka ake kalon lamarin ba? Malam Buhari Muhammad Darakta ne a cibiyar nazarin demukuraɗiyya da ake Abuja.

DW_Nigeria_Integration2
Hoto: Katrin Gänsler

"Tun daga farko da ma ba wai asalin mutane ne ke son waɗannan abubuwan ba manya ne suka zauna suka tsara suka hango za su ci gashinsu in har aka kawo waɗannan. Kamar in ka ɗauki batun 'yan sanda na jihohi in ka lura wacce jiha ce gwamna ba ya da ikon ya sanya 'yan sanda su yi abin da suka ga dama? Sannan batun janye kariya ga gwamnoni magana ce da take da kyau amma matsalar ita ce wannan ƙasar Najeriya, ko an cire kariya ko ba'a cire kariya ba ba zai canza komai ba. Ai Nuhu Ribado ya shaida mana cewa akwai gwamnoni wajen 35 da rigaya ya gano yana jiran su kamala wa'adinsu ne a kama su, amma ga shi sun gama mulkinsu ba kariyar ba komai amma har yanzu ba'a kama su ba."

To sai dai irin ra'ayoyin da ƙungiyoyin kare muradun mata suka gabatar sun sha bambam da na sauran al'umma musamman 'yan siyasa inda suka fi dagewa a kan batun gyara a kan wanene ɗan kasa a Najeriyar abin da ya sanya tambayar Hajiya Rabi Musa Abdullahi ta ƙungiyar kare muradun mata da nemo masu haƙƙi ta Wrapa ko menene dalilin hakan?

Ƙorafin ƙungiyoyin kare muradun mata

Duk da cewa tarurrukan da Majalisar wakilan Najeriya bisa radin kanta ta gudanar da su sun ba da dama ga 'yan Najeriya suka rarrabe aya da tsakuwa a kan irin wakilcin da wasu zaɓaɓɓun wakilai suke yi masu, lamarin da ya sanya wasu 'yan siyasa kasa halattar wuraren da aka gudanar da muhawara da ma gabatar da bukatun, abin da ya sanya Hajiya Rabi Musa Abdullahi ta ƙungiyar Wrapa da suka gabatar da muradunsu a wajen tarurrukan bayyana ƙorafi a kan lamarin.

DW_Delta8
Hoto: Katrin Gänsler

"Mata sun fi wahala a kan wannan saboda idan kina aure an ɗauko ki daga wata karamar hukuma ko jiha kin auri wani in kin zo kina neman tsayawa zaɓe sai a ce ai ke ba 'yar wannan jiha ba ce, kuma in kin koma a ce ke ba kin yi aure can ba, ya zamanto mace ta tashi a tutar babu ba ta nan ba ta can. Kuma mun gabatar da cewa a cikin kundin ba na maza ne kawai ba, domin duk inda ake magana sai a ce namiji-namiji, muka ce to a mai da shi ya kasance kowa na ciki har da maza da mata da ma naƙasasu."

A yayin da ake yaba wa ɗaukacin yadda aka gudanar da tarurrukan da a karon farko aka koma ga 'yan Najeriya don jin me suke so a gyara a tsarin mulkin ƙasar, abin jira a gani shi ne yadda 'yan majalisar za su tabbatar da sanya buƙatun zama dokoki da ka iya yin tasiri ga kyautata demukuraɗiyyar ƙasar da ke cike da ƙalubale da ma matsaloli na ci gaba.

Mawallafi: Uwais Idris Abubakar
Edita: Mohammad Nasiru Awal