1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhimmancin gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya ga Afirka

June 13, 2010

Gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya da muhimmancinta ga tattalin arziƙi da ma siyasar ƙasashen Afirka shi ne ya ɗauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/NpZy
An ƙaddamar da gasar cin kofin ƙwallon ƙafa a Afirka ta Kudu

A cikin nata sharhin ƙarƙashin taken: Gagarumin Biki ga Nahiyar Afirka, jaridar Die Zeit cewa tayi:

"Gasar ƙwallon ƙafa ta taimaka aka fara naƙaltar ainihin al'amuran Afirka a daura da matsaloli na yaƙe-yaƙe da cututtuka da cin hanci. Kimanin shekaru tamanin Afirka tayi tana zaman jira kafin yau a wayi gari tana karɓar baƙoncin gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya karo na farko a harabarta. Ke nako! wato lokaci yayi a harshen ƙabilar Bosotho. Abin nufi a nan kuwa shi ne lokaci yayi ga nahiyar Afirka."

Fußball WM 2010 Südafrika Mexiko
Gasa tsakanin Afirka ta Kudu da MexikoHoto: AP

Shi kuwa gwarzon namiji kuma tsofon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela cewa yayi wai yana ji kamar dai ya koma saurayi, kamar yadda jaridar Der Tagesspiegel ta rawaito, wadda tayi amfani da wannan dama don taɓo kaɗan daga cikin tarihin rayuwarsa sannan sai ta ce:

"Nahiyar Afirka ce wani dandali da ya rage na zuba kuɗi ba tare da haufi ba kuma mai yiwuwa gasar ta ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya ta ƙara taimakawa bisa manufa, saboda tuni dai aka fara samun canjin salon tunanin 'yan kasuwa na ƙetare dangane da wannan nahiya."

Ita ma dai jaridar Die Tageszeitung ko da yake ta nazarci gasar ta cin kofin duniya amma kuma taɓo taɓargazar gurɓata muhalli ne da ake yi a ƙasashen Nijeriya da Angola. Jaridar ta ci gaba da cewar:

Blick auf Ölförderanlagen im Nigerdelta
Rijiyar haƙan mai a Niger Deltan NijeriyaHoto: dpa

"A haƘƙiƙa abin dake faruwa a mashigin tekun Mexiko a halin yanzu haka, lamari ne da aka daɗe ana fama da shi a mashigin tekun Guinea. Rijiyoyin mai na Nijeriya a yankin Nigerdelta su ne akan gaba wajen gurɓata muhalli da haɗarurukan yoyewar ɗanyyen mai. A misalin shekaru 15 da suka wuce kamfanin Shell ta fuskanci taɓargaza a Nijeriya irin shigen wadda kamfanin BP ke fuskanta a yanzun a mashigin ruwan Mexiko.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Abdullahi Tanko Bala