1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mujallar Forbes ta baiyana waɗanda suka fi kuɗi a doron ƙasa

March 11, 2010

Carlos Slim na ƙasar Mexico ne mutumin da ya fi kuɗi a duniya.

https://p.dw.com/p/MPO0
Carlos SlimHoto: AP

Mujallar Forbes ta ƙasar Amirka ta baiyana sunayen mutane da suka fi kuɗi a duniya. Wani attajiri ɗan ƙasar Mexico da yayi fice a harkokin sadarwa mai suna Carlos Slim ne ya zo na ɗaya sakamakon marar zunzurutun ƙudi da ya zarta miliyon dubu 53 na dalar Amirka da yayi. Shi kuwa shugaban kanfanin Microsoft wato Bill Gates ɗan ƙasar Amirka ya zo a matsayi na biyu a bana. 'yan kasuwa biyu na ƙasar Indiya wato Mukesh Ambani da kuma Lakshmi Mittal suna a matsayi na hudu da kuma na biyar.  Mujallar ta Forbes ta ce idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, biliyoniya da duniyar nan tamu ta ƙunsa sun ƙaru duk da raɗaɗin koma bayan tattalin da wasu ƙasashe ke ci gaba da fiskanta. Mutane dubu da 11 ne suka mallaki kuɗin da ya tasamma miliyon guda na dalar Amirka a duniya, 62 daga cikinsu sun fito ne daga nahiyar Asiya. ƙasar China na a matsayi na biyu bayan Amirka na ƙasashen da suka fi ƙunsar attajirai a duniya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Edita: Yahouza Sadissou