1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jacob Zuma na cikin tsaka mai wuya

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 7, 2018

Shugaban jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu kana mataimakin shugaban kasa Cyril Ramaphosa ya gana da shugaban kasar Jacob Zuma

https://p.dw.com/p/2sGUR
Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu na cikin tsaka mai wuya
Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu na cikin tsaka mai wuyaHoto: Getty Images/S.Maina

Ramaphosa ya nunar da cewa suna tattaunawa tare da shugaban kasar Jacob Zuma da nufin ya mika mulki, wanda hakan ke zama wata babbar alama ta cewa Zuma zai yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda. Tattaunawar ta su dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Shugaba Zuma ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga al'ummar kasar na lallai sai ya sauka daga mukaminsa gabanin kammala wa'adin mulkinsa. Zuma dai ya samu kansa cikin wannan tsaka mai wuya ne bayan rahotannin cin hanci da rashawa da suka dabaibaye mulkin nasa.

A matsayinsa na mataimakin shugaban kasa kana shugaban jam'iyyar ANC, Ramaphosa zai maye gurbin Zuma da zarar shugaban ya sauka daga mukamin nasa. Mai shekaru 75 a duniya, Zuma ya kwashe tsahon shekaru tara yana mulkin Afirka ta Kudu, sai dai ya fara fuskantar matsala tun bayan da batun badakalar cin hanci da rashawa ya yi kamari a gwamnatina kana kuma ya fara fuskantar gagarumin kalubale na bukatar ya mika mulki tun bayan da Ramaphosa ya karbi ragamar shugabancin jam'iyyarsu ta ANC.